Ganduje yayi magana game nasarar da APC ta samu a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Kano

Ganduje yayi magana game nasarar da APC ta samu a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Kano

- Gwamnan jihar Kano yace nasarar da APC ta samu a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar ya nuna mutanen Kano suna goyon bayan gwamnatin sa

- Ganduje ya bukaci sabbin shugabannin kananan hukumomin jihar Kano da su yi koyi da gwamnatin jihar wajen yin ingatattun ayyuka a yankunan su

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, yayi bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 44 a jihar Kano a ranar Lahadi.

Ganduje yace nasarar da APC ta samu a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar ya nuna mutanen jihar sa, suna goyon bayan gwamnatin sa da jam’iyyar APC.

Da yake jawabi a lokacin bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi jihar a filin kwallon Sani Abacha, Ganduje ya bukace su da tabbatar da sun kawo wa yankunan su cigaba.

Ganduje yayi magana game nasarar da APC ta samu a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Kano
Ganduje yayi magana game nasarar da APC ta samu a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Kano

Ganduje yayi kira da su yi koyi da Gwamnatin jihar wajen gudanar da ayyuka masu inganci a kananan hukumomin su.

KU KARANTA : Mahauta 95 sun kamu da cutar Brucellosis a Bauchi

Gwamnan yayi wa shugabanin kananan hukumoni alkawarin basu goyo baya da hadin kai wajen sauke nauyin al'ummar yankunan su da ya rataya a wuyan su.

Ganduje ya bukace su da su ba hukumar sharia, jami’an tsaro da sarkunan gargajiya na jihar hadin kai dan kawo wa jihar Kano cigaba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: