Ina son zama soja domin fanshe kisan babana
Ibrahim Buppa, dan shekara 16 ya bayyana yadda yan Boko Haram suka kashe mahaifinsa.
Yana dan shekara 13 yan Boko Haram suka kashe mahaifinsa kuma har ila yau bai sanda inda mahaifiyarsa take ba.
Yayinda yake magana da jaridar The Cable a sansanin yan gudun hijran Gubio da ke Maiduguri, Ibrahim ya yi hawaye.
A shekara 16, kamata yayi ya shiga jami’a, amma har yanzu yana makarantan firamare.
A ranan da jaridar Cable ta kai ziyara sansanin, Ibrahim yace: “Ina jin dadin makarantan, ina son zama soja domin in yaka kuma in kashe Boko Haram.”
KU KARANTA: Bana son mijina, tursasani akayi na aureshi - Uwargida mai neman saki a kotu
Buppa yace a ranan da aka kashe mahaifinsa a Mayu 2015, yan Boko Haram sun shigo gidansa kauyen Jameri, karamar hukumar Bama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng