Sai Buhari ya koma PDP kafin na ba shi shawara- Lamido

Sai Buhari ya koma PDP kafin na ba shi shawara- Lamido

Rahotanni sun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ayyana cewa shi ba zai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar yadda zai magance wasu matsalolin da gwamnatinsa ke fuskanta ba har sai ya koma jam’iyyar PDP.

Majiyarmu ta rfi Hausa ta kawo cewa Lamido ya ce, matsalar cin hanci da rashawa ta fi tsanani a gwamnatin Buhari idan za a auna a mizai da tsohuwar gwamnati ta PDP.

A cewar Lamido sun tattauna da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da suka tabbatar mu su da irin sace-sacen da ake yi a gwamnatin Buhari.

Sai Buhari ya koma PDP kafin na ba shi shawara- Lamido
Sai Buhari ya koma PDP kafin na ba shi shawara- Lamido

Har ila yau tsohon gwamnan ya alakanta salon mulkin Buhari da damfara, musamman ganin yadda gwamnatin Buhari ta gaza magance matsalar tsadar kayayyaki duk da alamun da ta nuna na tinkarar wannan matsalar gabanin samun nasara a zaben 2015.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta gayyaci Oduah kan zargin karkatar da N3.6bn

Idan zaku tuna tsohon Gwamnan na Jigawa na daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkahsin inuwar jam’iyyar PDP a shekara mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: