Rashin lafiyar matar Zakzaky: Yaron El-Zakzaky ya rubuta doguwar wasika ga jami’an DSS da shugaba Buhari

Rashin lafiyar matar Zakzaky: Yaron El-Zakzaky ya rubuta doguwar wasika ga jami’an DSS da shugaba Buhari

Daya daga cikin yayan shugaban kungiyar shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, Mohammed Ibraheem Zakzaky, ya aika ma shugaban kasa wata doguwar budaddiyar wasika game da halin ni-yasun da iyayensa suke ciki.

Mohammed ya bayyana a cikin wasikar cewa baya ga shanyewar rabin jiki dake damun mahaifinsa, a yanzu haka mahaifiyarsa, Zeenatu Zakzaky na fama da Cutar Osteoarthritis.

KU KARANTA: Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun tsiya

Yaron yayi karin haske game da cutar kamar yadda Rariya ta ruwaito, inda yake cewa karancin bargon dake taimaka ma gwiwa ta yi aikinta yadda ya kamata ne ke janyo cutar, wanda hakan ke sanya mutum jin matsanancin zafi a duk lokacin da ya motsa gwiwarsa.

Rashin lafiyar matar Zakzaky: Yaron El-Zakzaky ya rubuta doguwar wasika ga jami’an DSS da shugaba Buhari
Matar Zakzaky

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mohammed yane fadin baya ga shanyewar rabin jiki dake damun mahaifinsa, a yanzu haka baya gani da idonsa na hagu, inda Idonsa na dama kuma ke cikin mawuyacin hali, wanda ta kai ga sai da gilashi yake amfani.

Idan za’a tuna a watan Disambar shekarar 2015 ne aka samu hatsaniya a tsakanin Sojoji dake rakiyar babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai da mabiya shi’a a garin Zariya, wanda yayi sanadiyyar mutuwar yan shi’a da dama, tare da kama shugabansu da matarsa.

Mohammed ya nuna takaicinsa game da rashin samun damar aikawa da kwararrun likitoci da zasu baiwa mahaifiyarsa cikakken kulawa, wanda yace hakan bai samu bane saboda muguntar gwamnati da hukumomin tsaronta.

Daga karshe yayi addu’ar Allah ya kawo karshen zaluncin Sojojin Nijeriya, da DSS, da kuma karshen mulkin Kama-Karyan Buhari, Shugaban Kasar da ke hana a yi wa mara lafiya tiyata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng