Mahauta 95 sun kamu da cutar Brucellosis a Bauchi

Mahauta 95 sun kamu da cutar Brucellosis a Bauchi

- Gwamnatin jihar Bauchi ta ce akalla mahauta 95 daga cikin mahauta 224 da aka yiwa gwaji a a asibiti suka kamu da cutar Brucellosis

- Dakta Istifanus Irimiya yace Daga jikin dabobi ake samu cutar Brucellosis

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce mahauta 95 suka kamu da cutar Brucellosis wanda ake samu da ga jikin dabobin gida.

Mataimakin Daraktan hukumar dake kula da lafiyar Dabobi karkashin ma’aikatan Noma da Ma’adanai na jihar Bauchi, Dakta Istifanus Irimiya, ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labaru a ranar Juma’a.

Dakta Istifanus Irimiya, yace daga cikin mahauta 224 dake garin Bauchi, da kananan hukumonin Misau, da Katagum, mahauta 95 suka kamu da cutar Brucellosis bayan am musu gwaji a asibiti.

Mahauta 95 sun kamu da cutar Brucellosis a Bauchi
Mahauta 95 sun kamu da cutar Brucellosis a Bauchi

Ya ce Brucellosis, cuta ce dake kama mutanen dake mu’amala da dabobi kamar mahauta, makiyaya da likitocin dabobi.

KU KARANTA : Zaben 2019: Bamu amince Amaechi ya kara zama Darekta janar na yakin neman zaben Buhari ba - Jiga-jigan APC

Yace ana kamuwa da cutan ne ta hanyar shan danyen nonon shanu da ba a dafa ba, cin danyen nama shanu, shan jinin dabobin dake dauke da cutar, da kuma rashin tsaftace wuraren ajiye dabobi.

“Alamun dake nuna mutum ya kamu da cutar ya hada da, zazzabi, ciwon kai, yawan yin zufa da dadare, da kuma sa masu juna biyu yin bari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: