Gwamnatin tarayya zata cigaba da yi wa 'yan Boko Haram 1,000 shari'a yau
- Gwamnatin tarayya zata cigaba da yi wa 'yan Boko Haram 1,000 shari'a yau
- Mai magana da yawun Ministan Mista Salihu Isah ya sanar da manema labarai hakan a jiya Lahadi
- Za'a cigaba da shari'ar ne a wani kebantaccen wuri a garin Kaiji dake a jihar Neja.
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ta hannun babban Ministan Shari'a na kasar Malam Abubakar Malami a yau Litinin ne za ta cigaba da yi wa 'yan Boko Haram din da ake zargi da kashe-kashe shari'a.
KU KARANTA: Jirgin Moscow yayi hatsari da mutane 71
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar damai magana da yawun Ministan Mista Salihu Isah ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jiya Lahadi inda ya bayyana cewa za'a cigaba da shari'ar ne a wani kebantaccen wuri a garin Kaiji dake a jihar Neja.
Haka zalika Malam Salihi Isa ya kuma bayyana cewa akalla wadanda ake tuhumar mutane 1,000 ne ake sa ran za a yi wa shari'ar kamar dai yadda kotun tarayyar ta umurta a watan Oktoban bara.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu da dumi-dumin sa na nuni ne da cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Benue ta sanar da gano biyu daga cikin jami'an ta hudu da suka bace a satin da ya gabata a wani kauye da ake kira Azage dake a karamar hukumar Logo a raye.
Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar mai suna ASP Moses Joel ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jiya da dare.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng