Harshen Hausa shi ne mafi karbuwa a cikin Nahiyar Afrika

Harshen Hausa shi ne mafi karbuwa a cikin Nahiyar Afrika

- Masu amfani da harshen Hausa sun yi zarra a kaf Duniya

- Yanzu haka akwai sama da mutane miliyan 150 da ke yaren

- Duk Afrika babu yaren da ya samu karbuwa irin na Hausa

Yanzu haka wani bincike da aka yi ya nuna cewa masu amfani da harshen Hausa na cikin wadanda su ka fi yawa a Duniya. Duk Afrika dama dai yanzu babu yaren da yayi fice irin na Hausa. Ana amfani da yaren a kasashen Nahiyar barkatai.

Harshen Hausa shi ne mafi karbuwa a cikin Nahiyar Afrika
Akwai sama da mutane miliyan 150 da ke Hausa

Spectator Index ta bayyana cewa wani nazari da aka yi ya nuna cewa sama da mutane miliyan 150 ke amfani da harshen na Hausa. Yaren dai shi ne na 11 cikin sahun wadanda su kayi fice a Duniya. Hausa na bayan irin su harshen Mandarin ne da Hindu.

KU KARANTA: Yawan Musulmai na karuwa matuka a fadin Duniya

Haka zalika an tabbatar da cewa akwai masu amfani da harshen Kasar Sifen da kuma Larabci da yaren kasar Rasha da duk sun sha gaban Hausa. Akwai kuma irin su Yaren Malay da Bengali na Yankin Asiya wanda su na gaban yaren na Hausa.

Hausa dai na bin bayan yaren Kasar Foshugal ne da kuma Faransanci. Amma masu yaren Hausa a Duniya sun kere yawan Jamusawa da mutanen Fashiya da kuma masu amfani da yaren Swahili na gida.

.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng