Tawagar fadan shugaban kasa sun halarci taron sadakan ukun mahaifin Janar Buratai
An gudanar da addu’oi a taron sadakan ukun marigayi Alhaji Yusuf Buratai, mahaifi ga Janar Tukur Buratai a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Gwamnan jihar Borno ya karbi bakuncin tawagar fadan shugaban kasa karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar Aso Rock, Abba Kyari, wadanda suka garzayo Maiduguri domin halartan taron sadakan ukun rasuwan mahaifin babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Y Buratai a yau Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2018.
Wadanda sukayi tattaki daga fadar shugaban kasa sune karamin ministan wutan lantarki, Sulaiman Hassan; sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Jalal Arabi, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Amb Babagana Kingigbe, mai magana da yawin shugaban kasa; Mal Garba Shehu, da sauran su.
Sauran jama’a masu karancin da suka halarci taron sun kunshi sarakuna, manyan jami’an gwamnati, yan uwa da abokan arziki, da al’umman gari.
KU KARANTA: Budurwa tayi watsi da bukatar auren saurayin da ya sadaukar da kodar sa domin ceton rayuwar ta
Zaku tuna cewa jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton rasuwan mahaifin Laftanan Janar Tuku Buratai ranan Juma’a 9 ga watan Fabrairu bayan gajeruwar jinya da yayi.
Allah ya jikansa da rahama, Amin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng