Wata sabuwa: Gwamnatin jihar Edo ta kafa dokar hana kiwo cikin dare
- Gwamnatin Jihar Edo ta hana yawon kiwo cikin dare dauke da makamai
- Mai magana da yawun Gwamnan Jihar, Cruso Osagie, shi ne ya bayyana hakan
- Osagie ya tabbarwa al'ummar Jihar samar da cikakkiyar tsaro
Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obasake, ya kafa dokar hana kiwo cikin dare dauke da makamai a Jihar. Gwamnan ya kuma kafa kwamitin mutane 8 don yin bincike game da rikici tsakanin Makiyaya da Manoma a Kananan Hukumomi 18 na Jihar.
Mai magana da yawun Gwamnan, Cruso Osagie, shi ne ya bayyana hakan a jiya. Ya ce Gwamnan ya kafa wannan doka ne bayan zantawa da ya yi da shuwagabannin Hausa/Fulani na Kananan Hukumomin Jihar.
KU KARANTA: Jama'a sun koka da jinkirin zuwan kayakin zaben Kananan Hukumomi a Kano
Osagie ya kuma bayyana cewar Gwamnatin ta hana bakin haure farauta a Jihar. Ya ce jami'ai daga Hukumomin tsaro mabambanta za su rinka shawagi na bazata. Duk wanda a ka kama dauke da makami zai fuskanci fushin Hukuma.
Obaseki ya kuma ce za a yi wa dukkan Makiyaya rajista ta yadda za a hada gwiwa da dukkan makiyaya a Kananan Hukumomin. Kwamitin za kuma ta rinka zantawa da wakilan Kananan Hukumomin bayan kowani watanni 3 don duba irin cigaban da a ka samu wurin kawo karshen rikicin.
A karshe, Obaseki ya yi kira ga jama'a da su rinka sanar da jami'an tsaro da bayanai da za su amfamar wurin shawo kan lamarin. Ya kuma tabbarwa jama'a samar ma su da cikakkiyar tsaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng