Rayuwa ta na cikin hadari, inji mai magana da yawun Babangida, Afegbua

Rayuwa ta na cikin hadari, inji mai magana da yawun Babangida, Afegbua

- Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida, Kazeem Afegbua ya ce rayuwarsa na cikin hadari

- Afegbua ya ce yana ta samun sakon kar ta kwana inda ake yin barazanar halaka shi da iyalan sa

- Hakan ne ya sa Afegbua ya ce zai mika rayuwarsa hannun gwamnatin tarayya har sai yadda hali ya yi

Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, Mista Kashim Afegbua ya ce rayuwar sa na cikin hadari tun bayan da ya wallafa sanarwan da tsohon shugaban kasan inda ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari ya hakura da batun neman takarar zabe a 2019.

Rayuwa ta na cikin hadari, inji mai magana da yawun Babangida, Afegbua
Rayuwa ta na cikin hadari, inji mai magana da yawun Babangida, Afegbua

Afegbua ya fadi wannan magana ne a zantawar da ya yi da manema labarai bayan ya baro ofishin yan Jami'an Binciken sirri na DSS da ke babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Dimokiradiyya har yanzu bata biya kudin ta ba a Najeriya - Jega

A cewar Afegbua, tun ranar Lahadi yana ta samun sakon kar ta kwana inda ake yi masa barazana kan rayuwarsa da na iyalan sa, wa su kuma na kallubalantar sa ya sake bayar da sanarwan kamar irin wadda ya bayar a baya.

Saboda hakan ne Afegbua ya yanke shawarar mika rayuwar sa hannun gwamnatin tarayya bai san abin da zai biyo baya ba.

Afegbua kuma ya koka kan yadda Hukumar ta DSS ke aika masa gayyata bayan gayyata duk da cewa ya amsa gayyatar su kuma ya rubuta cewa duk abin da ya fada umurni ne daga mai gidan sa tsohon shugaban kasa Badamasi Babangida.

A kwanakin baya, Legit.ng ta ruwaito inda rundunar yan sandan Najeriya ta gayyaci mai magana da yawun tsohon shugaban kasar Ibrahim Badamasi kan sanarwan da ya fitar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164