Shugaba Buhari ya aika sakon fatan alkhairi ga tawagar Najriya a gasar Olympics na 2018
- Shugaba Buhari ya aika sakon fatan alkhairi ga tawagar Najriya wanda ke kasar Koriya ta Kudu a yanzu haka domin gasar Olympics na 2018
- Wannan shine karo na farko da Najeriya zata kasance cikin wadanda zasu buga wasan Olympics din, sannan kuma shugaban kasar na alfahari da masu wakiltan kasar
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya aika sakon fatan alkhairi ga tawagar Najeriya wadanda ke wakiltan kasar a gasar Olympics wanda aka fara a ranar Juma’a, 9 gta watan Fabrairu a kasar Koriya ta Kudu.
Wannan shine karo na farko da Najeriya zata kasance cikin wadanda zasu buga wasan Olympics din sannan kuma shugaban kasar na alfahari da masu wakiltan kasar.
Shugaba Buhari ya yaba wa matan tawagar wadanda suka hada da Seun Adigun, Ngozi Onwumere da kuma Akuoma Omeoga bisa wannan gagarumin tarihi da suka kafa na kasancewa tawagar mata na farko a Afrika da zasu buga gasar Olympics a wannan rukuni.
Ya kuma yaba ma Simidele Adeagbo.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar kabilar Ibo na yunkurin haramtawa ‘yan uwansu cin naman Shanu
A baya Legit.ng ta rahoto cewa gasar Olimpics da za'a fafata a kasar Koriya ta kudu a bana, 2018, kasar ta Koriya ta cije ta qi amincewa a gina masallatai na wucin gadi domin samawa musulmi masu neman sauke faralli wuraren ibadunsu na yau da kullum.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng