Samar da 'yan sandan jihohi wani salo ne na raba kan Najeriya - Sheikh Sani Yahaya Jingir

Samar da 'yan sandan jihohi wani salo ne na raba kan Najeriya - Sheikh Sani Yahaya Jingir

- Shugaban majalisar malamai na Izala ya nuna adawa da kafa yan sandan jihohi

- A cewarsa hakan wani salo ne na raba kan Najeriya

- Ya shawarci gwamnatin tarayya da dunga bincike da kyau kafin daukar jami’an tsaro

Rahotanni sun kawo cewa shugaban zauren malamai na kungiyar Izala na kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir yayi adawa da kudirin kafa yan sandan jihohi.

A cewarsa hakan wani tsari ne na son raba kawunan Najeriya zuwa Kaman wata kasa-kasa.

Samar da 'yan sandan jihohi wani salo ne na raba kan Najeriya - Sheikh Sani Yahaya Jingir
Samar da 'yan sandan jihohi wani salo ne na raba kan Najeriya - Sheikh Sani Yahaya Jingir

Ya bayyana hakan ne a yayinda yake gabatar da wa’azi a masallacin Juma’a na Yantaya dake garin Jos.

KU KARANTA KUMA: Ba a yi mani adalci ba kan rikicin makiyaya da manoma — Buhari

Ya kuma yi kira zuwa ga gwamnatin tarayya da ta dinga bincike kafin daukar jami'an tsaron ta domin kaucewa daukar bara gurbi da kuma masu shaye-shaye.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike kan yadda jami'an rundunar ke gudanar da ayyukan su.

An bijiro da binciken ne domin gano ma'aikata cima zaune da kuma gurbatattun jami'ai cikin rundunar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng