EFCC za ta kara bankado bincike a kan tsaffin gwamnoni 14
- Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), za ta waiwayi tsaffin Gwamnoni bisa zargin sace kudaden al'umma
- Cikin wadanda za a waiwaya har da manyan jami'an gwamnati da iyalan su
- A na zargin su da sace kudin al'umma da ta kai naira biliyan 183
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), za ta kara bankado bincike a kan tsaffin gwamnoni 14 da wadansu manyan jami'an gwamnati da iyalan su bisa zargin handama da babakeren dukiyar talaka.
Jimmilin kudin har ya kai kimanin N183 biliyan. Jaridar Leadership Weekend ta yi tambihin cewa, Alkalain Alkalai na Kasa, Shehu Malami, ya bukaci takardun bincike a kan tsaffin gwamnoni 31 daga Hukumar EFCC da ICPC a watan Yuni na 2016.
KU KARANTA: Rashin Tausayi: Miji ya sayar da kodar matarsa a madadin kudin sadaki
Cikin su har da Bukula Saraki da Ali Modu Sheriff da Ahmed Sani Yeriman Bakura, Saminu Turaki, Adamu Mu'azu, Joshua Dariye, Peter Odili, Gabriel Suswan, Orji Uzor Kalu, Chimaroke Nnamani, Ikdei Ohakim, da Godswill Akpabio. Cikin manyan jami'an gwamnati kuwa akwai tsohon sifeta Janar na 'Yansanda, Tafa Balogun da wani Jigo na Jam'iyyar PDP, Bode Stelwart.
Bincike da shari'a a kan Balogun da Stewart ne kadai ya kamalla, a inda wata majiya ta ce ko shi din ma ba a wani zurfafa ba don kuwa da anyi tonon silili. Hakazalika, ba a bankado barayin kudaden 'yan fansho da na tallafin man fetur ba.
Majiyar ta shaida cewar nan ba da jimawa ba EFCC za ta waiwayo kan wadanda a ke zargi da laifukkan don tsananta bincike a kan su. Mun tattaro wannan labari me daga jaridar Leadership Weekend.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng