Hotuna: Jana'izar mahaifin Buratai
A safiyar yau ne jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton rasuwar Alhaji Yusuf Buratai, mahaifin shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.
Marigayi Alhaji Yusuf ya rigamu gidan gaskiya ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Legit.ng ta samu wannan rahoton ne da sanadin kakakin hukumar sojin kasa, Birgediya Janar S.K Usman, wanda ya shaidawa manema labarai a safiyar yau Juma'a, inda jiga-jigan gwamnatin kasar nan suka halarci jana'izar a birnin na Maiduguri.
KARANTA KUMA: Gobara: Wata yarinya ta dirgo daga gini mai hawa huɗu a jihar Abia
Mahaifin shugaban ssojin ya rasu ya bar 'ya'ya 14 da tarin jikoki, inda rahotanni suka bayyana cewa tsohon soji ne a lokacin samartaka ta rayuwar sa.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gobara ta lashe shagunan tafi da gidanka 30 a wata kasuwar wayoyin salula ta jihar Kano.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng