Ka nemi wata motar domin wannan ba za ta je ba - Fayose ya fadawa Ortom
- Ayodele Fayose yayi wa Ortom tayin PDP a Jihar Benuwe
- Gwamna Fayose ya fadawa Ortom ya fice daga motar APC
- Gwamnan Banuwe ya zargi Hukuma da sakaci wajen tsaro
Gwamnonin PDP sun fara kokarin zawarcin Gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom wanda a da tsohon ‘dan PDP amma yanzu yana cikin Jam’iyyar APC mai mulki. Kwanan nan dama Gwamna Wike ya kai masa ziyara har da gudumuwa.
Gwamnan Ekiti Ayodele Fayose ya ziyarci Jihar Benuwe idan ba ku manta ba inda yayi takwarar na sa tayin dawowa Jam’iyyar ta su. Ayo Fayose yace Jam’iyyar APC tayi watsi da Gwamna Ortom lokacin da yake neman taimako.
KU KARANTA: Ana zargin Makiyaya da kashe wani ‘Dan Sanda a Benuwe
Ayo Fayose ya zargi shugabancin APC daga mataki na sama ne da rashin agazawa Gwamnan lokacin da ake kashe dinbin jama’an Garin sa. A gaban jama’a dai Fayose ya fadawa Gwamna Ortom ya fita daga motar APC ya hau wata.
A cewar Fayose a kaikaice dai akwai motoci iri-iri don haka sai wanda ya zaba amma dai ya fada masa motar da yake tafiya ciki a yanzu ba za ta kai labari ba. Gwamna Ortom kuwa ya zargi Gwamnati da jami’an tsaro da sakaci a Jihar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng