Da dumi-dumi: Allah yayi wa mahaifin Janar Buratai rasuwa
Allah yayiwa Malam Yusuf Buratai, mahaifin babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya rasu
Malam Yusuf Buratai ya rasu ne a asibiti a Maiduguri.
Kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya bayyana hakan ga manema labarai da safen nan a garin Maiduguri.
Yace: “Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun. Mun sanar da ku rasuwan mahaifin babban hafsan sojin Najeriya, Alhaji Yusuf Buratai a Maiduguri.”
Wata majiya ta bayyana cewa marigayin ya kasance yana jinya a asibiti inda akayi masa aikin tiyata kafin rasuwansa.
KU KARANTA: Kwankwaso ya kaddamar yakin neman zabe, ya kai ziyara Anambara
Ya rasu ya bar ‘yaya 14 da jikoki da dama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng