Gobara ta lashe shaguna 30 a kasuwar wayoyin salula ta jihar Kano
Kimanin shagunan tafi da gidanka 30 ne suka suka salwanta a wata gobarar sassafiya da ta afku a kasuwar wayoyin salula ta Farm Centre dake tantagwaryar birnin jalla babbar hausa wato jihar Kano.
Kakakin hukumar 'yan kwana-kwana na jihar, Alhaji Sa'idu Muhammad, shine ya shaidawa 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Alhamis din da ta gabata, inda yake cewa gobarar ta afku ne da misalin karfe 1:55 na daren ranar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jami'in dan sanda, ASP Abba Sabo na ofishin 'yan sanda dake unguwar Kwalli, shine ya aika da kiran gaggawa ga hukumar ta kwana-kwana, inda cikin gaggawa suka aika da ma'aikatansu wannan kasuwa domin cika aikin da rataya a wuyansu.
Alhaji Sa'idu ya alakanta wannan tsautsayi da tangardar wutar lantarki, inda wayoyi suka game da juna a wani sashe na kasuwar.
KARANTA KUMA: Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta mayar wa shugaban NHIS kujerar sa
Ya kuma bai wa 'yan kasuwar shawarwari da mazauna yankin, akan kiyaye yadda suke mu'amalantar kayayyaki masu amfani da wutar lantarki domin gujewar afkuwar hakan a karo na gaba.
A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ma'aikata za su yiwa gwamnatin jihar Kano tawaye dangane da tatsar masu albashin su da take yi a kowane wata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng