Rikicin siyasa: An yi yunkurin tsige Shugaban Jam’iyyar APC a Bauchi
- APC ta karyata cewa an yi yunkurin tsige Shugaban ta a Bauchi
- Shugabannin Jam’iyya sun yi yunkurin tsige Shugaban na APC
- Sakataren APC mai mulki a Bauchi ya karyata wannan magana
Saura kiris a tsige Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Bauchi watau Uba Ahmed Nana kamar yadda labari ya zo mana a yau dinnan daga Jaridar Daily Trust. Sai dai Sakataren APC yace babu wanda ya isa ya cire Shugaban sai su.
Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Bauchi ta karyata rade-radin cewa wasu Shugabannin kananan Hukumomi 5 na Jihar karkashin jagorancin Rabiu Danbaba sun nemi sauke Shugaban su na Jihar Alhaji Uba Ahmed Nana daga kujerar sa.
KU KARANTA: 'Yan Majalisa sun nemi Ministan Buhari ya bayyana a gaban su
Shugaban Jam’iyyar a karamar Hukumar Garin Bauchi Alhaji Rabiu Shehu Danbaba yayi kokarin ganin an sauke Shugaban Jam’iyyar na Jihar da ga mukamin sa wanda ya sa Jam’iyyar ba tayi wata-wata ba ta kira wani taron musamman.
Manyan Jam’iyyar na Jihar daga kananan hukumomi 14 cikin 20 ne su ka zauna domin ganin ba a kai ga nasara ba. Sakataren Jam’iyyar a Jihar Haruna Disina ya bayyanawa manema labarai cewa babu maganar tsige Shugaban na su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng