Dan Majalisar Tarayya ya mallakawa kungiyar Izala katafaren Masallacin da ya gina (hotuna)
- Dan majalisa yayiwa kungiyar Izala kyautar azo a gani
- Ya mallakawa kungiyar wani katafaren masallaci da ya gina a jihar Plateau
Wani dan majalisar tarayya, Ahmad Idris Maje ya mallakawa kungiyar Izala wani katafaren masallaci da ya gina a jihar Plateau.
Ahmad ya kasance an majalisa dake wakiltan mazabar karamar hukumar Wase na jihar Plateau a majalisar dattawa.
Ya mallakawa kungiyar Izala wacce hedkwatar ta ke a garin Jos babban birnin jihar Plateau masallacin.
An gina masallacin ne a yankin Bashar na karamar hukumar Wase.
Ga hotuna a kasa:
KU KARANTA KUMA: Badakalar kudade: An gurfanar da dan tsohon gwamna a gaban kotu a jihar Kano
A baya Legit.ng ta kawo cewa an gurfanar da dan tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, Nuraini Adamu tare da wani mutun mai suna Felix Onyago a gaban wata kotun tarayya dake garin Kano.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng