Zidane ya yanke shawarar yin bankwana da kungiyar Real Madrid

Zidane ya yanke shawarar yin bankwana da kungiyar Real Madrid

- Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, ya yanke shawarar ajiye aikinsa

- Zidane ya yanke wannan shawara ne biyo bayan rashin nasarar da kungiyar Real Madrid ke fuskanta a cikin gasar cin kofina daban-daban da take bugawa

- Jaridar wasanni a kasar Sifen ta bayyana cewar Zidane ya zabi ajiye aikinsa ne a kan hukumar kungiyar ta kore shi

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Sifen, Zinedine Zidane, ya yanke shawarar ajiye aikinsa a karshen kakar wasanni ta bana.

Zidane ya yanke shawarar ya mika takardar barin aiki a maimakon ya fuskanci korar kare daga hukumar kungiyar ta Real Madrid.

Zidane ya yanke shawarar yin bankwana da kungiyar Real Madrid
Zidane ya yanke shawarar yin bankwana da kungiyar Real Madrid

Osinbajo ya goyi bayan kirkirar 'Yan Sandan Jihohi

Wata jaridar wasanni a kasar Sifen, Don Balón, ta rawaito cewar Zidane ya dauki wannan mataki ne saboda rashin nasara da kungiyar ke fuskanta a gasar cin kofina daban-daban da take bugawa a bana duk da cewar kwangilar sa a kungiyar sai 2020 zata kare.

Mahukuntar kungiyar Real Madrid basu kalubanci ko yunkurin hana Zidane barin kungiyar ba, wani al'amari dake nuni da cewar suma basa farinciki da halin da kungiyar ta fada.

Ya zuwa yanzu babu labarin ko kungiyar ta fara neman wanda zai maye gurbin Zidane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: