Osinbajo ya goyi bayan kirkirar 'Yan Sandan Jihohi

Osinbajo ya goyi bayan kirkirar 'Yan Sandan Jihohi

- Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana goyon bayan sa kan batun bawa johohi izinin kafa Yan sandan su

- Osinbajo ya ce hakan ne yafi dacewa da Najeriya idan akayi la'akari da cewa yan sandan da kasar ke dashi sunyi karanci

- Yayi wannan maganar ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da Majalisar Dattawa ta shirya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana goyon bayan sa kan batun kirkiro 'Yan sandan jihohi inda ya kara da cewa hakan ne abin da yafi dace wa da Najeriya.

A jawabin da yayi a taron samar da tsaro da Majalisar Dattawa ta shirya, Osinbajo ya ce adadin Yan Sandan da Najeriya ke dashi ba za su iya samar da tsaro a dukkan fadin kasar ba, hasali ma dacewa yayi a rubunya adadin su sau uku.

Osinbajo yana goyon bayan kirkiro 'Yan Sandan Jihohi
Osinbajo yana goyon bayan kirkiro 'Yan Sandan Jihohi

Ya kuma jawo kan hankalin mahalarta taron kan hadin gwiwa tare da kasashen da Najeriya ke makwabtaka da su domin inganta tsaron. Osinbajo har ila yau, ya gargadi masu ruwa da tsaki a fanin tsaron su guji alakanta matsalolin tsaron da addini.

KU KARANTA: Ana samar da megawatt 94,627 na lantarki a kullum cikin watanni 4 na karshen shekarar 2017 - NBS

A yayin da yake tofa albarkacin bakin sa, Shugaban Majalisa, Bukola Saraki ya yi juyayin yadda al'amuran tsaron suka tabarbare a sassan kasar inda makwabta ke kaiwa juna hari, ya kuma ce ya zama dole a dauki mataki domin kawo karshen matsalar.

A jawabin da ya yi, Jagoran masu rinjaye, Ahmad Lawan ya ce taron na cikin gudunmawar da Majalisar ke bayar wa ne wajen ganin cewa an kawo karshen rikice-rikicen da suka barke a wasu sassan kasar.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito yadda Yan sanda a jihar Ondo suka ceto wasu mutane uku daga hannun yan fashi da sukayi garkuwa da su a hanyar su na zuwa Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164