Wata sabuwar kungiya (Sabon alfijir a siyasar Najeriya) karkashin jam'iyyar PDP ta kudiri kawo canji na gaskiya

Wata sabuwar kungiya (Sabon alfijir a siyasar Najeriya) karkashin jam'iyyar PDP ta kudiri kawo canji na gaskiya

- Kungiyar ta kira kanta da sabuwar alfijir din siyasar Najeriya da zata tsayar da dan takara mai nagarta

- Sun bayyana cewar dan takarar su ba zai kasance mai kabilanci ko nuna wariya ga wani yanki, kabila, ko addini ba

- Sun bukaci 'yan Najeriya da kada su karaya ko fitar da rabo daga samun canji na gaskiya

Wata kungiyar siyasa da ta kira kanta da suna 'sabuwar alfijir' a siyasar Najeriya karkashin jam'iyyar PDP ta ci alwashin kawo canji na gaskiya ta hanyar fitar da dan takara nagari da zai wakilci jam'iyyar a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Kungiyar ta ce ta kafu ne domin tabbatar da cewar jam'iyyar PDP ta fitar da dan takara mai nagarta da zai samu goyon bayan dukkan 'yan Najeriya.

Wata sabuwar kungiya (Sabon alfijir a siyasar Najeriya) karkashin jam'iyyar PDP ta kudiri kawo canji na gaskiya
PDP ta kudiri kawo canji na gaskiya

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran kungiyar, Imade Ize-Iyamu, ya aike wa da Legit.ng ya ce zasu tabbatar da cewar dan takarar da jam'iyyar PDP zata fitar a zaben shekarar 2019 bai kasance mai kabilanci ko nuna wariya ga wani yanki, kabila, ko addini ba.

DUBA WANNAN: Akwai munafurci da rashin da'a a wasikun IBB da Obasanjo ga Buhari

Kungiyar bata bayyana wanne dan takara take goyon baya ko take muradin ganin jam'iyyar ta tsayar takara ba. Illa iyaka dai ta ce dan takarar da zasu goya wa baya zai kasance yana da gogewa da kuma ilimin tattalin arziki.

Kungiyar ta bayyana kwarin gwuiwar da take da shi na cewar dan takarar su zai sharewa 'yan Najeriya hawayensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng