Bidiyon yadda wani jirgin yakin soji ya tarwatsa wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram

Bidiyon yadda wani jirgin yakin soji ya tarwatsa wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram

- Hukumar sojin Najeriya na cigaba da zafafa yakin da take yi da mayakan kungiyar Boko Haram

- Ko a karshen makon jiya saida dakarun sojin suka ragargaji mayakan kungiyar a wata maboyar su, kamf zero, dake dajin Sambisa

- A jiya Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, ya fitar da wani faifan bidiyo yana mai bayyana cewar ya gaji da wannan masifa

Hukumar sojin Najeriya na cigaba da zafafa yakin da take yi da 'yan kungiyar ta'addanci ta boko haram kamar yadda Legit.ng ke kawo maku rahotanni a kullum.

A yayin da a jiya, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ke bayyana cewar ya gaji da masifar da dakarun sojin Najeriya suka saka kungiyar sa, sai ga shi hukumar sojin sama ta kasa ta fitar da wani faifan bidiyo da yake nuna yadda dakarun hukumar suka kai hari tare da lalata wata maboyar kungiyar Boko Haram.

Bidiyon yadda wani jirgin yakin soji ya tarwatsa wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram
Jirgin yakin sojin sama ya tarwatsa wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram

Hukumar sojin saman ta bayyana cewar jirginta na yaki (RPA) ya lalata wata motar yaki ta kungiyar Boko Haram a daf da dajin Sambisa.

DUBA WANNAN: Shekau ya bayyana a sabon faifan bidiyo, ya musanta ikirarin hukumar soji

Jirgin ya hangi motar yakin 'yan ta'addar ne yayin da yake shawagi a sararin samaniyar dajin Sambisa da kewaye kuma bayan sanar da ofishin hukumar ne aka turo jirgin yaki RPA da ya yi ruwan wuta a kan mayakan kungiyar da motar su.

Sanarwar da Olatokunbo Adesanya, darektan hulda da jama'a na hukumar sojin sama ta kasa, ya fitar ta tabbatar da cewar sun kone motar yakin 'yan ta'addar kurmus tare da lalata maboyar mayakan kungiyar.

Ku kalli faifan bidiyon a nan:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: