Zaki ya kashe mai kula da shi a jihar Kaduna

Zaki ya kashe mai kula da shi a jihar Kaduna

- Mutumin da zaki ya kai ma hari a gidan shakatawa na gamji Gate dake jihar Kaduna ya mutu

- Mutane sun shiga rudani a jihar Kaduna yayin da wani zaki ya kufce daga dakin da aka killace shi a ranar Asabar

Mai kula da namun daji da wani zaki ya kai wa farmaki a ranar Asabar a gidan shakatawa na Gamji gate dake Kaduna ya mutu.

Marigayin mai suna, Mustafa Adamu, ya mutu ne tsa sanadiyar raunakan da ya samu a yayin da zakin ya yagalgala shi bayan ya kufce daga kejin da aka killacce shi a gidan zoo na Gamji gate.

Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawito labarin yadda al'amarin ya faru a ranar Asabar a filin shakatawa na Gamji Gate, inda mutane da dama suka tsallake rijiya da baya sakamakon kufcewar zakin.

Zaki ya kashe mai kula da shi a jihar Kaduna
Zaki ya kashe mai kula da shi a jihar Kaduna

A jawabin da mamacin ya yi kafin ya mutu, ya ce zakin ya samu kufcewa ne bayan ya kammala ba shi abinci a ranar Asabar da misalin karfe 12 na rana inda yayi kuskure ya bar wani waje da ya kamata rufe a buda sai kawai zakin ya sulalo ya fito waje.

KU KARANTA : 'Sojoji na kuntatawa mutane a kudancin Kamaru'

"Daga fitowar sa sai ya yiwo kaina ya turmushe ni, sai abokan aikina suka ankara suka yi wa zakin tsawa, sai ya fice a guje.

"Sai na ji abokan aikin na sun fara salati, nima sai na fara amsa wa. Daga wajen suka garzaya dani asibiti."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: