Majalisar Wakilai ta umurci Sifeta Idris ya roki gafarar Gwamna Ortom
- Majalisar ta umurci Sifeta Ibrahim Idris na Hukumar 'Yansanda ya nemi afuwan Gwman Ortom
- Majalisar ta kuma bukaci a sauke Mashood Jimoh, mai magana da yawun Hukumar daga bakin aikin sa
- Ta yi wannan umurni saboda furicin da Sifetan ya yi a kan Ortom, ta bakin Jimoh
Majalisar Wakilai ta umurci Sifeta Ibrahim Idris na Hukumar 'Yansanda, da ya roki gafarar Gwamnan Jihar Benue, Ortom, bisa ikakarin sa na cewa Ortom mutum ne da ke nitsewa.
Ta yi wannan umurni ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabarairu bayan kwamitin kula da Lamurran Hukumar 'Yan Sanda na Majalisar ta gabatar da sakamakon binciken ta ga Majalisar.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya canja salon addu'ar da ake yi a zaman sati-sati na majalisarsa
Akasarin 'Yan Majalisar sun yi tir da wannan furuci na Sifetan. Majalisar ta kuma bukaci a sauke Mashood Jimoh a matsayin sa na mai magana da yawun Hukumar, don ta bakin sa ne furucin ya fito.
Kafin zaman Majalisar da ta bayar da wannan umurni, 'Yan Majalisun na Jihar Benue sun yi taron manema labarai a inda su ka bukaci a sauke Jimoh daga kan aikin sa. Majalisar sai ta ga bukatuwar jin ta bakin ko wani bangare kafin zartar da hukunci.
A baya, Legit.ng ta ruwaito ma ku cewar sakamakon haka ne Majalisar ta bukaci Kwamitin ta mai kula da harkokin Hukumar 'Yansanda da sauran Jami'an Tsaro da ta yi bincike kan lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng