Umrah: Mata na kokawa kan goge da ake yi musu yayin dawafi
- A yayin ibada a Makka ana gwamutsa ne mata da maza
- Wajen dawafi yamutsewar na fin karfin masu agaji
- Wasu mata sun labarta yadda mazan banza ke musu goge da lalube yayin ibada
A yayin ibada a harami, wuri yakan yamutse, mata da maza, manya da yara, inda ake sa rai kowa ya riga ya tsarkake kwakwalwarsa daga batsa ko sha'awa, domin neman falala da tsarkakuwa ga ubangijinsa, sai dai ba haka abin yake ba a gaske.
Karin mata, da ke da bakin iya fadi, na gabatowa da batun an musu kutse a lamarinsu, inda ake musu goge, ko cacuma, da ma keta haddi yayin aikin ibadarsu, a wurare masu tsarki, musamman a haramin Makka.
Tsiyar lalatar mutanen banzan taffi yawaa a wurin tawafi, inda a nan ne ake samun cakuduwa da turereniya, da ma aringizo, inda wasu ke yi da gangan domin neman laushi.
A yannzu dai, mata na ffitowa su ffadi irin takaici da keta haddi da suka shiga, yayin irin wannan katsa-landan da shaidanu keyi, a gaban ka'aba, ba kunya ba tsoron Allansu, balle tawaalu'u.
DUBA WANNAN: Aso Rock ta ce ta samar da ayyuka har miliyan 7
Wannan tonon silili na abin kunya ya faro ne a yanar gizo, inda wata maniyyaciya, Sabika Khan, 'yan asalin Paskitan, ta bayyana irin zullumi da ta shiga bayan wani janibi yayi mata gogen rashin mutunci, sau fiye da ukku.
Daga nan sai abin ya fara bazuwa, inda mata da yawa suma suka fito fili domin fadin irin nasu abin haushin da ya same su yayin sauke faralli.
Ga dukkan alamu dai, hukumomin kasar ta Saudiyya basu san ana wannan ta'asa ba, in ko sun sani, lallai an sansu da daukar danyeen hukunci kan masu keta musu hududin kasarsu ta shari'ar Islama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng