Hankalin fasinjoji ya tashi yayinda kofan jirgi ya balle
Hankalin fasinjojin jirgin Dana Air ya tashi yayinda kofan jirgin ya balle daga sauka a filin jirgin sama.
Daya daga cikin fasinjojin mai suna Dapo Sanwo, yace kofan da ya balle dama a kwance yake tun lokacin da suka hau jirgin wanda ke nuni ga cewa ba’a kula mai kyau.
Wani fasinjan mai suna, Ola Brown, ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa abin ya tayar masa da hankali.
“Ina kusa da gaban jirgin da na ji karan faduwar kofan, da farko sha nike tashin bam ne. Ban taba tunanin kofa ne ya fadi ba.”
KU KARANTA: Bamu yarda da Zina da duk wani aikin alfasha a dakunanmu ba - Cewar wani Otel a jihar Gombe
Yayinda jaridar Premium Times ta tuntubi kamfanin Dana Air da safiyan nan, sunce sai sun saurari jawabin injiniyoyinsu kafin su yi magana akan al’amarin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng