Yadda wani tsohon janar na rundunar Sojan sama yayi amfani da matarsa suka yi watandan naira miliyan 4,000
A cigaba da shari’ar tsohon shugaban shugaban hafsan hafsoshin rundunar sojan Najeriya, Alex Badeh dangane da tuhume tuhumen da hukumar yaki da rashawa, EFCC ke yi masa, an gano wata sabuwa.
A yayin sauraron karar a ranar Talata 6 ga watan Feburairu, inda lauyan Badeh ya yi tambayoyi ga shaidan hukumar na goma sha tara, Abubakar Madaki, jami’in hukumar EFCC, wanda ya bayyana cewar tare da abokan aikinsa, sun gano miliyoyin nairori da Alex Badeh ya sata da sunan iyalinsa.
KU KARANTA: Hattara dai: Daga tambayar ranar aurensa, wani matashi ya harzuka ya kashe matambayin
Premium Times ta ruwaito Madaki ya shaida ma Kotu cewar asusun bankin Zenith, inda Badeh ke antaya kudaden rundunar Sojin Najeriya a ciki, na matarsa ne, Mary Badeh, ya kara da cewa asusun dake dauke da sunan kamfanin Iyalikam an bude shi ne da sunan Mary a ranar 23 ga watan Yuni na shekarar 2004.
Hakazalika majiyar Legit.ng ta ruwaito shaidan EFCC ya cigaba da tona asirin Badeh, inda yace wani kamfani ma da Badeh ya saci kudaden al’umma ta cikinta mai suna ‘Prince and Princess’, shi ma mallakin iyalansa ne, gaba daya daraktocin kamfanin iyalansa ne, a nan ma, Matarsa Mary Badeh ce ta bude asusun kamfanin a banki.
Bayan lauyan Badeh ya kammala tambayoyinsa ga shaidan hukumar EFCC, wanda ya fara tun watanni shidda da suka gabata, tare da samun amsoshin tambayoyinsa, lauyan EFCC, O.A Atolagbe ya mika ma Kotu bukatar a dage sauraron shari’ar, don ya yi nazarin hujjojin da shadan su ya bayar.
Daga karshe, Mai shari’a Abang ya dage sauraron karar zuwa ranar 26 da 28 ga watan Maris.
Idan za’a tuna, tun bayan sauyin gwamnati, inda shugaban kasa Muhammadu Buhai ya kayar da Gooluck Jonathan ne aka fara gudanar da binciken yadda aka kashe kudaden makamai da kuma kudaden rundunonin Sojojin Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng