Matsalar Tsaro: Gwamna El-Rufai ya koka kan matsalar tsaro a yankin arewa
- El-Rufai ya kokan kan matsalar tsaro
- Sarkin Anka ya kawo wa El-Rufai ziyara a Kaduna
- An bukaci sarakunan gargajiya su bada hadin kai domin kawo karshen matsalar tsaro a arewa
Gwamna Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana rashin tsaro a yankin arewa a matsayin babban kalubalen da ke bukatar manyan shugabannin arewa su shiga domin warwarewa.
Ya fadi hakan a ranar Talatar nan, a ofishin sa, lokacin da yake karbar bakunci ziyarar da wata tawagar mutanen jihar Zamfara suka kawo mishi. Tawagar wanda ta sami jagorancin, Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad.
El-Rufai ya bayyana rashin tsaro a wannan yankin a matsayin abin hadari wanda ake bukatar hadin gwiwar sarakunan gargajiya domin warware matsalar.
DUBA WANNAN: Sokoto: Tambuwal yayi wa gwamnatin sa garambawul
Sarkin wanda ya jagoranci tawagar ya yi jawabi cikin rashin nuna jin dadi, game da sace - sacen mutane, da shanu, da wasu 'yan bindiga suke yi a jihar ta Zamfara da sauran yankunan arewa a kasar nan.
Yace akwai bukatar a sake tsarin hukumomin tsaro a kasar nan, domin magance matsalolin da suke damun yankunan na arewa. Sarkin ya yi kira ga gwamnan da ya hada kai da sarakunan gargajiya na jihar domin kawo karshen tashe - tashen hankalin.
Yace ziyarar ta su zuwa Kaduna sunyi ta ne, don gano hanyar da za abi domin magance matsalar tsaro a fadin kasar nan, kuma ya roki gwamnonin arewa dasu ba da hadin kai domin kawo karshen matsalar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng