Dandalin Kannywood: Adam A. Zango ya daura damarar yaki da wasu 'yan masana'antar fim
- Adam A. Zango ya daura damarar yaki da wasu 'yan masana'antar fim
- Yace dukkan bara gurbi da kuma gurbatattun masana'antar su ta shirya fina-finan Hausa su shirya fada da shi
- Ya yi wannan aman wutar ne a jiya
Fitaccen jarumin nan na wasannin Hausa a masana'antar Kannywood kuma shahararren mawakin Hausa na zamani watau Adam A. Zango ya fito karara ya bayanna cewa shi fa ya daura aniyar yaki da dukkan bara gurbi da kuma gurbatattun masana'antar su ta shirya fina-finan Hausa.

KU KARANTA: Nayi hannun riga da Kwankwaso har abada - Ganduje
Jarumin ya yi wani dogon bayani ne ba tare da kama suna ba a shafin sa na dandalin sada zumunta na Instagram inda ya bayyana cewa shi ba da abokin aikin sa Ali Nuhu yake fada ba amma da gurbatattun 'yan masana'antar ta su yake wadanda ya bayyana su da mutane da masu jin tsoron Allah.
Legit.ng dai ta samu cewa jarumin haka zalika ya bayyana cewa daga yanzu zai rika fede biri har wutsiyar sa a kan dukkan abubuwan da yaga suna faruwa a masana'antar da bai gamsu da su ba a cikin wata sabuwar makala da ya sanyawa suna 'Gyara Kayan ka'.
Haka kuma a karshen bayaninsa ya ce "Na sani ba Lallai in zauna lafiya ba. Kuma na sani za'a iya neman rayuwata amma duk da haka NA BAYAR DA RAINA"
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng