Hattara dai: Daga tambayar ranar aurensa, wani matashi ya harzuka ya kashe matambayin

Hattara dai: Daga tambayar ranar aurensa, wani matashi ya harzuka ya kashe matambayin

Wani al’amari mai cike da abin mamaki da tausayi ya faru a kasar Indonesiya, inda wani matashi ya halaka wata mata mai dauke da juna biyu a ranar 19 ga watan Janairu na shekarar 2018.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a unguwar Kampung Pasir dake jihar Jonge na kasar Indonesiya

KU KARANTA: Wani shahararren ɗan fashi da makami ya bada kai bori ya hau bayan fuskantar matsin lamba daga Sojoji

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a wata rana wani matashi mai suna Faiza Nurdin mai shekaru 28 na zaman zamansa a kofar gida, sai makwabciyarsa mai suna Aisyah mai shekaru 32 ta zo wucewa ta gabansa, inda bayan gaisawa ta tambaye shi ‘wai sai yaushe zaka yi aure?’.

Hattara dai: Daga tambayar ranar aurensa, wani matashi ya harzuka ya kashe matambayin?
Matashi Faiz

Ashe wannan tambayar bata yi ma Faiza dadi ba, inda shi a nasa jawabin a gaban Kotu yace Aisyah ce masa ta yi “Kayi kayi kai aure, abokanka na ta aure, kai kuwa kana nan zaune.”

Wucewar Aisyah gida kenan ke da wuya, sai Faiz ya kama hanya zuwa gidan matar, da ta fito falo don ta ga bakonta, sai Faiz ya tare ta, inda ta koma cikin dakinta, shi kuwa ya bita hark an gadonta, ya makare mata wuya har sai da tace ga garinku nan.

Hattara dai: Daga tambayar ranar aurensa, wani matashi ya harzuka ya kashe matambayin?
Lokacin da yake aikata laifin

Yansanda sun tabbatar bayan Faiz ya kashe matar, sai ya dauke wayarta da kuma makudan kudi da suka kai RM 230, kuma ya tsere zuwa unguwar Kalideres na birnin Jakarta.

Sai dai abinka da kwararrun Yansandan kasar Indonesiya, sai da suka kwakulo wannan mai laifi, har suka ji masa rauni da bindiga a kafarsa, inda ake tuhumar Faiz da laifin kisan kai, kuma zai iya fuskantar hukuncin kisa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: