Dandalin Kannywood: Fim ya fi aikin soja wahala – Inji Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Fim ya fi aikin soja wahala – Inji Rabi'u Rikadawa

Shahararren tauraron nan na fina-finan Hausa Rabi'u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya ce aikin soja ya fi fim sauki.

A cewar jarumin idan mutun na fitowa a matsayin jarumi baya samun lokaci na kansa da zai ce harma zai hada fim nasa na kansa.

Inda ya jaddada cewa harkar fim ya fi na soja wahala domin su sojoji akan samu ranar da suke hutu basa kan aiki.

Ya ce shi yanzu yana zaune ne a Kaduna, amma cikin shekaru bakwai ba zai iya tuna yaushe ya shafe kwanaki bakwai a Kano ba.

Dandalin Kannywood: Fim ya fi aikin soja wahala – Inji Rabi'u Rikadawa
Dandalin Kannywood: Fim ya fi aikin soja wahala – Inji Rabi'u Rikadawa

Kullun suna wajen hada fim, kuma basa samun isasshen lokaci nasu na kansu har sai sun kammala shirin fim da suke kai.

Ya kuma bayyana cewa yana fitoiwa a fina-finan kudu, kuma akan sa su yin al’adu da ba nasu ba kuma ace sai sun yi.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Allah ya yiwa tsohon mijin Sadiya Gyale rasuwa

Daga karshe yace a jaruman yanzu babu mai burgesa kamar Adam Zango, domin tamkar shi yake duk irin mataki da aka daura shi yana hawa da kyau.

A halin da ake ciki Legit.ng ta kawo cewa tsohon mijin shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Sadiya Gyale wato Alhaji Abubakar Muhammad ya amsa kiran mahallicin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng