An nada wadanda za su yi wa Atiku kamfe na zaben 2019 a Kudancin Najeriya
- Wata Kungiya ta shirya kawowa Atiku Kasar Inyamurai a 2019
- Atiku Wazobia tace babu wanda ya dace da kasar nan illa Atiku
- Kungiyar tace Atiku Abubakar bai da nuna bambanci a tafiyar sa
Yanzu haka mun samu labari cewa yakin neman zaben Shugaban kasa na tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Atiku Abubakar ya ratsa Yankin Kudu maso gabashin Najeriya inda su kace ba ya nuna bambanci a shugabancin sa.
Jagoran Kungiyar Atiku Wazobia Gabriel Churchill Chukwuemeka da yake jawabi a Jihar Imo ya bayyana cewa Najeriya yanzu na bukatar mutum ne irin Wazirin na Adamawa wanda bai da son rai da fifita mutanen sa wajen shugabanci.
KU KARANTA: An roki Shugaban kasa Buhari ya hakura da tazarce a 2019
Churchill Chukwuemeka ya nuna cewa za su kawowa Atiku Abubakar Yankin na Kudu maso gabashin kasar nan idan aka fito zaben 2019. A cewar jagoran tafiyar na Wazobia, Atiku ya dace da kasar nan don kuwa ya san sha’anin mulki.
Har ma dai wannan mutumi ya bayyana sunayen wadanda za su jagoraci yakin neman zaben Atiku a Yankin a Jihohin Anambra, Ebonyim Abiya, da Enugu wadanda su ka hada da; Emeka Charles, Uche Umazi, Kanayo Afunugo, da Ikechukwu Ohanedo
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng