Nan bada jimawa ba zan wancakalar da jajayen huluna na – Gwamna Ganduje

Nan bada jimawa ba zan wancakalar da jajayen huluna na – Gwamna Ganduje

Tirka tirkan siyasar jihar Kano ta dauki wani sabon salo inda giwayen dake fafatawa a cikin wannan takaddama, tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje suka raba gari na dindindin.

Daily Nigerian ta ruwaito gwamna Ganduje na fadin cewar shi da Kwankwaso har yauma taqumus sa’a babu sulhu a tsakaninsu, ya bayyana haka ne kuwa a yayin wani taron ganawa da yan takarkarun jam’iyyar APC a zabukan kananan hukumomin dake karatowa a jihar.

KU KARANTA: Gwamnatin kasar Birtaniya ta fara binciken kadarorin Bukola Saraki masu darajar fam miliyan 15

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamnan yana cewa tsagin Kwankwasiyya na jam’yyar APC ta shirya fada da tsagen Gandujiyya, ta hanyar shigar da kara a Kotu suna bukatar a dakatar da zaben kananan hukumomin da zai gudana a ranar 10 ga watan Feburairu, don haka yace a shirye yake ya maida biki.

Nan bada jimawa ba zan yi wancakalar da jajayen huluna na – Gwamna Ganduje
Kwankwaso da Ganduje

“Kowa ya san cewa bamu da hakkin ya Kwankwasiyya, ina mamakin yadda suke yayatawa cewa ba zamu ci zabe ba tare da da su ba, alhalin wannan maganan karya ce, don haka daga yau mun raba jihar da Kwankwasiyya har abada.

“Don kuwa yan Kwankwasiyya basa ganin kokarin da muke yi game da wannan zabe, ban taba ganin kiyayya irin wannan ba, amma wai suna kiran a azo ayi sulhu, sulhun me kuma? Idan aka yi sulhu, ya zamu yi da jar hula? Ni kai na na kusan cire tawa.” Inji shi

Tsatstsamar dangantaka tsakanin Ganduje da Kwankwaso ya faro ne tun bayan da Ganduje ya dare madafan iko, shi kuwa Kwankwaso yayi kokarin mallake jam’iyyar APC a jihar, wayon da Ganduje bai yarda da shi ba kenan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng