Rashin lafiya gadan-gadan ta sanya alƙali ya ɗaga shari'ar Sanata Goje

Rashin lafiya gadan-gadan ta sanya alƙali ya ɗaga shari'ar Sanata Goje

Shari'ar da aka shafe shekaru shidda ana gudanarwa dangane tuhumar EFCC akan zambar kudi ta tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Danjuma Goje, ta sake samun tsaiko a yayin da rashin lafiya gadan-gadan ta riski alƙali mai shari'a, Babatunde Quadiri a ranar talatar da ta gabata.

Hukumar EFCC tana zargin Goje, wanda ya aikata laifin zamba a yayin da yake gwamnan jihar Gombe, inda ya wuwushe N25bn tare da hadin gwiwar wasu mutane uku makarraban gwamnatin sa.

Sanata Danjuma Goje
Sanata Danjuma Goje

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, an fara gudanar da shari'ar ne da misalin ƙarfe 9:05 na safiyar yau talata a babbar kotun tarayya ta biyu dake birnin Jos a jihar Filatu, inda rashin lafiya ta riski mai shari'a Quadiri da ya sanya babu makawa a dakatar da shari'ar.

KARANTA KUMA: Amfani 8 na ruman ga lafiyar ɗan Adam

Legit.ng ta fahimci cewa, rashin lafiya ta cimma mai shari'ar ne inda yayi wani dogon tari mai tsanani da ya sanya ya kirayi lauyoyin ɓangarori biyu har fadarsa domin zayyana musu halin da ake ciki tare ɗage sauraron ƙarar zuwa ranakun 10 da 11 na watan Afrilun 2018.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobbi akan hare-haren makiyaya da 'yan ta'adda a yayin ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Nasarawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng