Yadda Jigawa tayi zarra wajen noman zobo a Gwamnatin Buhari
- Jihar Jigawa tayi fice wajen harkar noman zobo a Najeriya
- A bara kurum an fita da zobo na sama da Dala Miliyan 35
- Sauran Jihohin Arewa sun dage wajen harkar noman zobo
Mun samu labari cewa yanzu maganar da ake yi Jihar Jigawa tana samun makudan Miliyoyin Dalolin kudin shiga daga harkar gona musamman a harkar noman ganyen sobo watau zoborodo.
Jaridar Daily Nigerian ta kawo rahoto cewa, ta harkar fita da zobo zuwa kasashen waje, Jihar Jigawa ta samu sama da Dala Miliyan 35 a cikin watanni 9. Kungiyar NAQS mai duba lafiyar kayan gona a Najeriya ta bayyana wannan a Abuja.
KU KARANTA: Buhari ya nemi a rika fifita Najeriya wajen bada kwangila
A bara jihar Jigawa ta fitar da ganyen zobo zuwa Kasar Mexico da yah aura na Dala Miliyan 20. Bayan nan kuma kasashe da dama na neman ganyen na zobo saboda irin amfanin sa wajen yin kayan dadi da kuma yin magununa a Duniya.
Sauran Jihohi irin su Zamfara, Katsina, Kano, Kebbi, Borno da Yobe ba a bar su a baya ba wajen noman zobo. Zai dai yi wahala zobo yayi a Kudancin kasar saboda yanayin garuruwan. Masana dai sun nuna cewa zobo na da amfanin gaske.
Ku na da labari Aliko Dangote ya horas da mutane 150 a Kasar Indiya. An tura mutanen ne horo a kasar waje domin shiryawa Kamfanin Dangote da zai fara aiki nan gaba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng