Rikicin Benuwe : IG ya tura rundunonin ‘yansada na musamman jihar Bneuwe
- Sifeto janar na 'yansanda ya tura rundunonin ‘yansanda na mussaman guda 15 jihar Benuwe
- Kwamishinan 'yansadan jihar Benuwe ya ce jami'an su a shirye suke su fatattaki masu ta da zaune tsaye a jihar Benuwe
Sifeto Janar na ‘yansanda, Ibrahim Idris, ya tura rundunonin ‘yansanda na mussaman guda 15 jihar Benuwe dan kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar
Kwamishinan ‘yansandan jihar Benuwe, Fatai Owoseni, ya bayyana haka a ranar Litinin a lokacin da yake zantawa da manema labaru birnin Makurdi.
“Babban burin sifeto janar na ‘yasandan Najeriya shine kawo karshen kashe-kashen da ake yi a fadin kasar.
“Wannan shine dalilin da yasa ya turo mana rundunoni ‘yansanda na musaman dan taimakawa jami’an mu dake nan," inji Owoseni.
KU KARANTA : Kashi 70% daga cikin fursunonin dake jiran kotu ta yanke musu hukunci satar rake da doya suka yi – Abubakar Malami
Ya ce an samu zaman lafiya a kauyen Yogbo, kuma an tura jami'an ‘yansanda kananan hukumomin Kwande, Agatu, Gboko, Makurdi, Buruku, Katsina-Ala, Gwer West da Vandeikya.
Kwamishinan ya tabbatar da ceto dansandan da ya bace a lokacin da makiyaya suka kai wa garin Yogba dake karamar hukumar Guma hari a watan Faburairu.
Owoseni yace rundunar su ashirye suka su fatattaki masu ta da zaune tsaye a jihar Benuwe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?
Asali: Legit.ng