Rigimar Siyasa: Mutum biyar sun jikkata a rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya
- Mutane biyar ne suka ji rauni a rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya
- An kone shaguna a garin Talatar - Jido a karamar hukumar Dawakin Kudu
- Anyi taron kungiyar Gandujiyya a kauyen Talatar - Jido
Wasu mutane biyar sun ji rauni jiya a Talatar-Jido a garin Dawakin Kudu na jihar Kano, bayan rikici tsakanin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da magoya bayan, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Mun samu rahoton cewa, sun yi amfani da da makamai suka dinga saran junan su, kuma suka kone shaguna da dama a Kwanar Talatar Jido.
Wani shaida, Abdulmajid Garba Jido, ya ce fadan ya samo asali ne, bayan wasu 'Yan Gandujiyya sun fito daga taron su da misalin karfe 2 na rana, a kauyen Talatar - Jido. "Inda wani mai neman takarar shugaban karamar hukuma na yankin yazo yake ganawa da magoya bayan sa, bayan sun gama ganawa sun fito sai suka ci karo da 'Yan kungiyar Kwankwasiyya, inda fada ya kaure tsakanin kungiyoyin biyu. Inda mutane biyar suka ji raunuka, sannan suka kone wasu shaguna."
DUBA WANNAN: Siyasa: Bayero Nafada ya sake watsi da taron APC a jihar Gombe
Ya kara da cewar daga baya aka garzaya da wadanda aka yiwa raunin asibi mafi kusa, domin yi musu magani. Da aka tuntube shi DSP Magaji Musa Majia, ya ce yana Abuja, yana yin wani aiki, amma zai tuntubi mutanen shi ta waya, domin jin yadda abin ya wakana.
Wannan fadan dai ba wai shine na farko ba a tsakanin kungiyoyin biyu, tun lokacin da suka samu rabuwar kai. Ya taba faruwa a Kofar Kudu lokacin Hawan Daushe, shekarar data gaba ta, inda mutane da yawa suka ji ciwo, ciki kuwa hadda tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dokta Rabi'u Sulaiman Bichi.
Sannan kungiyoyin sun kara haduwa wata daya daya wuce, a wurin biki, a Chiranchi Kano, wasu sun ji rauni a lokacin, ciki hadda 'Yan uwan Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Abdullahi Abbas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng