Har yanzu akwai sauran aiki gaban Jami'an tsaro a Borno inji Sanatan Jihar
- Ministan tsaro yace an ci karfin kaf ‘Yan Boko Haram a Borno
- Dan Ali yace babu yankin Borno a hannun ‘Yan ta’adda yanzu
- Wani Sanatan Borno yace ba za ace an gama da ‘Yan ta’adda ba
Mun samu labari cewa Sanatan Jihar Borno ta Arewa Abubakar Kyari ya karyata Ministan tsaro Birgediya Janar Mansur Dan Ali (Mai ritaya) game da maganar da yayi na cewa an gama da ‘Yan Boko Haram a Jihar gaba daya a wani taro.
Jaridar Daily Nigerian ta rahoto Sanata Abubakar Kyari yana cewa Garin Marte wanda yana cikin inda yake wakilta har yanzu ta na hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram. Sanata Kyari yace dole sai an kara dagewa wajen ceto mutanen mazabar ta sa.
KU KARANTA: Gwamnan Jihar Kuros-Ribas ya yabawa Shugaban kasa Buhari
Sanatan ya bayyana cewa ko da an yi galaba kan ‘Yan Boko Haram, amma har yanzu ayyukan kasuwanci da sauran sha’anin rayuwa ba su dawo daidai ba tukuna saboda yadda ‘Yan ta’addan na Boko Haram su kayi wa Yankin a kwanakin baya.
Ministan tsaro dai yayi ikirarin cewa yanzu haka babu wani yanki ko bangare na Jihar Borno da ke hannun ‘Yan Boko Haram. Rundunar Sojoji sun ce bam-baman da aka dasa ne ya hana mutanen Marte komawa gidajen su daga inda su ke gudun hijira.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng