Ba mu taba amfana da Gwamnati kamar ta Buhari ba – Gwamna Ayade

Ba mu taba amfana da Gwamnati kamar ta Buhari ba – Gwamna Ayade

- Gwamnan Jihar Kuros-Ribas ya yaba da mulkin Shugaba Buhari

- Ben Ayade yace Shugaban kasa Buhari bai nuna masu bambanci ba

- Mutanen Jihar Kuros Ribas sun samu mukamai a Gwamnatin nan

Mun ji cewa Gwamnan Jihar Kuros-Ribas Ben Ayade, duk da yana Jam’iyyar adawa ta PDP ya yabawa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace sun ci moriyar inda su ka samu ruwan mukamai duk da bambancin su.

Ba mu taba amfana da Gwamnati kamar ta Buhari ba – Gwamna Ayade
Ben Ayade ya yabawa Gwamnatin Shugaban Buhari

Gwamna Ben Ayade yake cewa duk da Shugaba Buhari Musulmi ne kuma ‘Dan Yankin Arewa, amma ba a taba samun lokacin da Jihar Kuros-Ribas ta more ba kamar a Gwamnatin Buhari inda su ka samu mukamai birjik.

KU KARANTA: Wani tsohon Gwamnan Kudu yayi zanga-zanga a Najeriya

Yanzu haka dai Shugaban Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ta fito ne daga can, haka kuma Shugaban Hukumar NDDC da kuma Shugaban Hafsun Sojin ruwan Najeriya. Bugu da kari ma dai Alkalin Alkalai ya fito ne daga Jihar.

Ayade yace a wannan Gwamnatin su na da Ministan Neja-Delta gaba-daya da kuma Odita-Janar na kasa. Bayan Shugaba Buhari ya hau mulki kuma dai Jihar Kuros-Ribas ya fara ziyara duk da irin banbancin da da su ke da shi.

Labari ya zo mana a jiya cewa wani Babban Malami na addinin Kirista a kasar nan ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Nija Babangida Aliyu ne zai karbi mulkin kasar daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng