Ba sasanta Kwankwaso da Ganduje ya kai ni Jihar Kano ba – Osinbajo
- A karshen makon nan Osinbajo ya halarci daurin aure a Kano
- Mataimakin Shugaban kasa yace ba siyasa ta kai shi Garin ba
- Farfesa Osinbajo yace biki aka yi sannan ya kuma gaida Sarki
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa sam bai shiga cikin rikicin siyasar Jihar Kano da ake ta faman tafkawa tasakanin Sanata Rabi’u Kwankwaso da magahin sa wartau Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba.
Farfesa Yemi Osinbajo yayi karin haski game da ziyarar da ya kai a karshen makon nan inda aka ji ya gana da manyan Jihar. Osinbajo ta bakin mai magana da yawun sa yace babu abin da ya hada ziyarar sa da maganar siyasa illa daurin aure da ya zo.
KU KARANTA: Mutane 3000 sun tsere daga PDP zuwa Jam’iyyar APC
Laolu Akande ya fitar da jawabi daga fadar Shugaban kasa inda yace daurin aure ne kurum ya kai Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo. Wani Hadimin Farfesa Osinbajo mai suna Kwamared Hafiz Kawu ne yayi aure a Kano a karshen makon da ta wuce.
Akande yace maganar ace ya je sasanta rikicin siyasar Jihar ba gaskiya bane. Osinbajo dai ya hadu da Gwamna Ganduje ne a filin jirgi wanda daga nan ya zarce Masallaci aka daura aure, sannan kuma ya gana da Sarki kamar yadda aka saba a al’ada.
A da mun rahoto cewa Sanata Kabiru Gaya da kuma Sanata Barau Jibrin su na cikin wadanda su ka gana da Mataimakin Shugaban kasar. Osinbajo dai yace sam ba maganar siyasa ta kawo sa Jihar ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng