Wani Mutumi zai leka cikin sama domin gano fasalin Duniya
- Wani Mutumi zai leka sararin samaniya domin ganin fasalin Duniya
- Wannan Ba-Amurke dai bai yadda cewa Duniyar nan ba a kife ta ke ba
- Don haka yace dole ya je ya ganewa kan-sa da kan-sa ya huta da karya
Wani Bawan Allah zai leka zuwa sararin samaniya shi kadai kwanan nan domin ganewa kan sa gaskiya game da yadda wannan Duniyar da Bil Adama da sauran halittu su ke raya ta ke.
Mun samu labari daga Jaridar Independent ta kasar waje cewa Mike Hughes, wani Bawan Allah a Amurka na shirin ganewa kan sa siffar Duniyar da mu ke rayuwa inda ya nuna rashin amincewar sa ga binciken da masana su kayi.
KU KARANTA: Yaron Shehi Dahiru Bauchi ya kafirta wasu 'Yan Darika
Wannan mutumi dai ya dage domin ganin ya cin ma burin sa na zaam sama-jannati. A da dai Jama’a sun yi gardamar cewa jirgin da ya hada ba zai tashi ba. Gwamnatin Kasar sa ma dai tayi kokarin taka masa burki inda tace bai da hurumi.
Hughes ya bayyanawa manema labarai cewa zai tafi zuwa wajen Duniyar da ‘yan kallo domin a haskawa Jama’a. Shi dai wannan mutumi bai yadda cewa Duniya ba a kife ta ke ba don haka ya shirya neman kudi da halin da zai gani da idon sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng