An fara sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje

An fara sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje

- Tun bayan kammala zaben shekarar 2015 aka fara takun saka tsakanin Sanatan Kano ta tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso, da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje

- Rikicin siyasa tsakanin aminan junan biyu ya kara lalacewa bayan da gwamnatin jihar ta hana Kwankwaso yin taron ganawa da magoya bayansa a jihar

- Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin sulhunta sabanin dake tsakaninsu

Tun bayan kammala zaben shekarar 2015 aka fara takun saka tsakanin Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ga zababben gwamna, Abdullahi Umar Ganduje.

Masana harkar siyasar Kano sun ce rikici tsakanin aminan junan ya fara ne saboda tsoma baki ciki sha'anin mulkin jihar da tsohon gwamna ya yi, zargin da kwankwaso da magoya bayansa suka sha musantawa.

An fara sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje
Kwankwaso da Ganduje

Dangantaka tsakanin 'yan siyasar biyu ta kara rubewa ne bayan da magoya bayan Kwankwaso suka yi zargin cewar gwamna Ganduje ya yi amfani da hukumar 'yan sanda wajen hana Kwankwaso yin taron ganawa da magoya bayansa a jihar.

Ganin al'amarin na daukar wani sabon salo ne ya saka gwamnatin tarayya shiga tsakani domin yin sulhu a tsakani.

DUBA WANNAN: An kuma: Tsohon shugaban kasa IBB ma ya aike da tasa budaddiyar wasikar ga shugaba Buhari

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gana da Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje a fadar gwamnati dake Abuja kafin daga bisani su kara yin wata ganawar a karshen makon jiya yayin da shi Osinbajo ya halarci wani daurin aure a jihar Kano.

Ana saka ran shigar fadar shugaban kasa cikin rikicin zai kawo karshen sabanin da ya shiga tsakanin wasu siyasar biyu.

Kamar yadda Legit.ng ta kawo maku rahotanni a kan dambaruwar siyasa tsakanin Kwankwaso da Ganduje, yanzu ma zamu ci gaba da kawo maku daki-daki yadda sulhun ke gudana

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: