Abba Kyari ya yiwa gwamnatin tarayya kakkausar suka akan karancin albashin da ake biyan ‘yansanda

Abba Kyari ya yiwa gwamnatin tarayya kakkausar suka akan karancin albashin da ake biyan ‘yansanda

- Abba Kyari ya bayyana damuwar sa akan karancin albashin da 'yansadar Najeriya kai karba

- Kyari yace 'yansadar kasashen da ba su kai Najeriya arziki ba sun fi 'na Najeriya karban albashi mai tsoka

Mataimakin kwamishinan‘yansanda kuma shugaban rundunar ‘Intelligence Response Team (IRT) Abba Kyari, ya bayyana damuwar sa akan karancin kudin da ake daukar nauyin rundunar ‘yansadan Najeriya.

Kyari wanda ya shahara bayan ya kama gawurtaccen mai garkuwa a mutane, Chukwudi Onuamadike, wanda aka fi sani da Evans jihar Legas, ya ce albashin da ake biyan ‘yansandan Najeriya yayi kadan kuma basu da makaman aiki kamar yadda yakamata.

Kyari ya bayyana haka ne a shafin sa na Facebbok a lokacin da yake jimamin bakin cikin mutuwar wani sajent mai suna, Tom Mohammed, da masu garkuwa da mutane suka kashe shi.

Abba Kyari ya yiwa gwamnatin tarayya kakkausar suka akan karancin albashin da ake biyan ‘yansanda
Abba Kyari

Kyari ya ce, Sajent Tom Mohammed, yana cikin rundunr IRT da suka hana masu garkuwa da mutane sace wani bature a jihar Nasarawa.

KU KARANTA : Kudin fansho: Maina ya maka mukaddashin shugaban hukumar EFCC a Kotu

Kyari ya ce, ‘yansadar kasashe kamar, Kenya, Benin, Colombia da basu kai Najeriya arziki ba sun fi ‘yansadar Najeriya karban albashi mai tsoka.

Abba kyari yace, yana da tabbacin cewa albashin ‘yansadar kasar zai karu da zarar majalissar wakilai ta amince da kudirin 'Police Trust Fund Bill' da aka gabatar mata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng