Rikicin makiyaya da manoma: Ganduje ya miƙa ma Makiyaya goron gayyata zuwa jihar Kano
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yayi kira ga Fulani makiyaya, musamman wadanda ke fuskantar kalubale da matsaloli game da kiwonsu a duk fadin kasar nan da su dawo jihar Kano don samun mafaka.
Ganduje ya bayyana cewa bai ga dalilin da manoma zasu dinga rikici da makiyaya ba, har ace ana rasa rayuka, alhali kuwa jihar Kano na da makeken fili da zai ishi dukkanin makiyayan, inji rahoton Premium Times.
KU KARANTA: Waiwaye adon tafiya: Gwamna Ganduje ya tuna lokacin da yake kiwon shanu (Hotuna)
“Ina kira ga makiyayan Najeriya da su dawo jihar Kano, akwai isashshen wuraren kiwo da zai ishi shanu fiye da miliyan daya, a Garun Malam, Kura, Rogo, Gaya, Ungogo da Tudun wada, inda duk akwai laba na kiwon dabbobi.” Inji Ganduje.
Gwamnan ya bayyana haka ne a sakamakon rikita rikitan da ake yawan samu a tsakanin makiyaya da manoma a sassan kasar nan, wanda ya janyo asarar rayuka da dama, wanda hakan ya janyo kaddamar da dokar hana kiwo a jihohin da suka hada da Benuwe, Taraba da Ekiti.
Sai dai kungiyar Fulani makiyaya, Miyetti Allah ta yi watsi da bukatar gwamnan jihar, inda shugaban kungiyar reshen jihar Benuwe, Haruna Ubi ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa shawarar da gwamnan ya bayar ba zai yiwu ba.
“Ai akwai yan kabilar Tibi a jihar Kano, shin suma zasu koma garuruwansu ne? mun gode ma gwamnan, amma gaskiya ba zamu iya barin jihar Benuwe ba ko sauran garuruwan da Fulani suke zaune ba , don wasu muggan dokoki da ake kaddamarwa.” Inji shi.
A wani labarin kuma, ana cigaba da tattuna matsalar dake haifar da rikici tsakanin makiyaya da manoma don ganin an shawo kan matsalar musamman a jihohin Taraba, Nassarawa, da Benuwe.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng