Sabon Rahoto: 'Yan Najeriya N100,000 ne ke kamuwa da cutar Kansa a duk shekara
- Cutar Kansa ko daji, batta da magani, sai dai sa'a
- Ana kokarin gwaji don gano ta da wuri, kafin ta fara yawo
- A Afirka, kasashe 28 bassu da ko inji daya na kone cutar
A sabon rahoto da aka fitar daga majalisar dinkin Duniya, A Najeriya, da kasashen dake Afirka, jama'a da yawa na kamuwa da cutar kansa.
Sabon rahoton da WHO ta fitar dai, ya nuna cewa, sama da mutum 100,000 ke kamuwa da cutar ta kansa a kowacce shekara, a Najeriya kadai, kuma akalla a kullum maza 40 ke mutuwa, da mata 25, daga cutar ta kansa a kasar.
DUBA WANNAN: Kar ku zabi Buhari a 2019
A dai sabuwar kididdigar, akwai kasashen nahiyar Afirka akalla guda 28 wadanda bassu da ko inji daya na maganin cutar.
Wannan na nufin babu damar da masu cutar zasu iya yin gwaje-gwajen cutar ko maganinta balle ma su sami kulawa ta gari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng