Gara Jam’iyyar PDP da APC mai mulki Inji Jam’iyyar adawa

Gara Jam’iyyar PDP da APC mai mulki Inji Jam’iyyar adawa

- Jam’iyyar adawa ta PRP tayi kaca-kaca da Jam’iyyar APC

- Shugaban PRP yace babu bambanci tsakanin PDP da APC

- PRP tace dole a takawa APC da ma PDP burki a zaben 2019

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta gamu da suka daga daya daga cikin manyan Jam’iyyun adawa a kasar nan watau PRP. Jam’iyyar tace APC tarin mayaudara ne irin PDP.

Gara Jam’iyyar PDP da APC mai mulki Inji Jam’iyyar adawa
Ashe gara PDP da APC inji Jam’iyyar adawa ta PRP

PRP ta koka da mulkin APC inda tace gara ma Jam’iyyar PDP da aka karbi mulki daga hannun su. Jam’iyyar ta PRP tace APC ta danne kowa a kasar nan kuma ana neman a danne sauran ‘Yan siyasa a Najeriya a mulkin APC.

KU KARANTA: Jama’a sun gaji da APC sun kosa a koma Jam’iyyar PDP

Shugaban Jam’iyyar rikon kwarya na PRP a Jihar Kwara Farfesa Mahmood Aliyu ya bayyana wannan kwanaki. Farfesan yace kusan tafiyar APC da PDP duk daya ce inda ‘ya ‘yan ta su ke sauya sheka a siyasa bini-bini.

Aliyu ya koka da yadda Gwamnatin Buhari ta rika saba umarnin kotu wajen shari’ar Sambo Dasuki da irin su Ibrahim Zakzaky. APC tace dole a takawa PDP da APC burki a zaben 2019 domin a ceci ‘Yan Najeriya daga zalunci.

Kun ji cewa Injiniya Buba Galadima wanda yana cikin amintattun Jam’iyyar APC yayi kira ga ‘Yan Najeriya su fita su shiga Jam’iyyar NRM.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng