Wani Limami da wasu mutane 8 sun dirka wa wata 'yar shekara 13 ciki
- Wata yarinya mai shekaru 13 da ake zargin wani Limami da wasu mutane 8 da yiwa fyade na dauke da juna biyu na tagwaye
- Shugabar wata gidauniyar taimako (Arridah) Malama Rabi Salisu, ce ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN)
- Limamin da ake zargi na daga cikin wadanda suka aikata wannan abin kunya, makwabcin su yarinyar ne
Wata yarinya mai shekaru 13 kacal a duniya da ake zargin wani Limami da wasu mutane 8 da yiwa fyade, yanzu haka na dauke da cikin 'yan tagwaye.
Shugabar wata gidauniyar taimako (Arridah) Malama Rabi Salisu, ce ta sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) wannan labari bayan an kawo masu yarinyar domin neman agaji.
Malama Rabi ta ci alwashin hada karfi da kungiyoyin kare hakkin mata da kananan yara domin ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan abin kunya.
Malama Rabi ta bayyana takaici da mamakinta bisa faruwar wannan al'amari.
"Mutum takwas fa! a kan yarinya mai shekaru 13, adadinsu kadai ya isa ya cutar da yarinyar domin ko nono babu a kirjinta, bata kai ga budurci ba ma" inji Malama Rabi.
DUBA WANNAN: Mai duba lafiyar matar Shekau ta saduda, ta mika wuya ga jami'an tsaro
Wani bincike da NAN ta gudanar ya nuna cewar Limamin da ake zargi na daga cikin wadanda suka yiwa yarinyar ciki, makwabcinsu ne.
Wannan abin takaici da ban haushi ya faru ne a karamar hukumar Ikara dake jihar Kaduna.
Tuni dai mahaifin yarinyar, Malam Mu'azu Shitu, ya maka wadanda ake zargin gaban wata kotun shari'ar musulunci dake Ikara.
Dukkan mutanen da ake zargi sun musanta yin lalata da yarinyar.
Saidai yarinyar da bakinta, ta bayyana cewar su na bata dari biyar ne kafin suyi lalata da ita sannan su gargadeta cewar kada ta sake ta fadawa kowa tare da yi mata barazanar kisa idan suka ji zancen a bakin wani.
Lamarin fyade na neman zama ruwan dare a fadin Najeriya domin kusan kullum ka ziyarci shafin Legit.ng zaka samu labarin wani ya aikata laifin fyade.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng