Dakarun Soji sun kwace makamai masu yawa, sun kubutar mutane 84 daga hannun kungiyar Boko Haram

Dakarun Soji sun kwace makamai masu yawa, sun kubutar mutane 84 daga hannun kungiyar Boko Haram

- A kalla mutan 84 sojin Najeriya suka kubutar daga hannun mayakan bokoharam a jiya, Asabar

- Shugaban rundunar ofireshon Lafiya dole, manjo janar Rogers Nicholas, yace wasu matan da aka kubutar na dawke da juna biyu

- Hukumar Soji ta tabbatar da cewa, zata kaddamar da wasu sabbin atisaye "harbin kunama 111, da crocodile smoke 111, da Kuma Egwu Eke Dance 111 a shekarar nan

A Kalla mutan 84 sojin Najeriya suka kubutar daga hannun mayakar Boko Haram a ranar asabar da ta gabata. Rundunar sojin tace, tayi nasarar ne ayayin wani hari da ta kai dajin Sambisa a jihar Borno.

A jumulance mutane 84 mayakan Boko Haram suka yi garkuwa dasu a sansaninsu na kamf zero, kafin sojin ta kubutar da su sannan ta mika wa cibiyar bayar da agajin gaggawa ta jihar borno (SEMA).

Shugaban rundunar ofierashon Lafiya dole, Manjo Janar Rogers Nicholas, yace wasu matan da aka kubutar na dauke da juna biyu, sannan yaran kuma nada karancin koshin lafiya. Ya Kara da cewa, mafi yawancinsu na dandanon 'yanci a cikin shekaru uku.

Dakarun Soji sun kwace makamai masu yawa, sun kubutar mutane 84 daga hannun kungiyar Boko Haram
Wasu mata da aka kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram

Akalla mayakan kungiyar Boko Haram 26 ne suka mika wuya ga rundunar sojin dake karaman hukumar Damboa a ranar jumua aka bayanar da tubabbu boko haram a meduguri, tareda makaman su, wanda ya hada da RGPs.

DUBA WANNAN: Mai duba lafiyar matar Shekau ta saduda, ta mika wuya ga jami'an tsaro

An jikkata akalla mutum 25,000 daga 2009 zuwa yanzu, sannan akalla mutum miliyan biyu da rabi na sansanin 'yan gudun hijira a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe. Hukumar Soji ta tabbatar da cewa, zata kadamar da ayyukan rundunar na "harbin kunama 111, da crocodile smoke 111, da Kuma Egwu Eke Dance 111 a 2018.

Rundunar harbin kunama 1 da 2 an kadamar dasu ne a shekarun 2016, da 2017, don kawar da matsalar rikicin satar shanu, da kuma fada tsakanin makiyaya da manoma, a arewancin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: