Gwamnatin Jihar Katsina za ta dauki Malaman asibiti aiki
-Ana shirin a dauki Malaman asibiti 600 aiki a Katsina
- Gwamnan na kokarin gyara harkar lafiya a fadin Jihar
- Gwamnatin Jihar ta dauki Ma’aikatan lafiya kwanaki
Labari ya zo mana cewa Gwamnan Jihar Rt. Hon. Aminu Bello Masari zai dauki ma’aikatan asibiti a fadin Jihar wannan shekarar domin inganta harkar kiwon lafiya a Jihar Katsina.
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Aminu Masari ta sanar da cewa za ta dauki unguzoma 600 aiki a fadin Jihar. Bayan nan kuma za a dauki Likitoci har 54 domin ganin an gyara sha’anin kiwon lafiya.
KU KARANTA: Gwamna Masari zai kashe Biliyan 15 wajen titi
Bayan wannan kuma har yau, Gwamna Masari yayi alkawarin daukar sauran Ma’aikata da za su taimaka wajen aikin asibiti a asibitocin Jihar. Yanzu haka Gwamnan yace an rage fita waje domin ganin Likita a Jihar.
Idan ba a manta ba kwanakin baya Gwamnatin Jihar ta dauki Ma’aikatan lafiya. Yanzu haka dai an gyara wasu asibitoci inda wasu irin asibitin Rimi aka sa kayan aiki na zamani domin duba marasa lafiya a Katsina.
Kwanan nan kun ji cewa Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari zai kashe makudan kudi wajen yin hanyoyi a fadin Jihar Katsina.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng